Gwamnatin Najeriya ta karbi dala miliyan 52.88 daga kadarorin Galactica da aka kwato daga Amurka, wadanda ake dangantawa da tsohuwar ministar albarkatun man fetur Diezani Alison-Madueke.
Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’ar Najeriya Lateef Fagbemi ne ya bayyana hakan yayin bikin rattaba hannu a kan yarjejeniyar kwato kadarorin tsakanin Najeriya da Amurka a Abuja a yau Juma’a.
Da yake gabatar da jawabinsa Fagbemi ya bayyana cewa za’a tura dala miliyan 50 daga cikin kudin da aka kwato zuwa aikin samar da lantarki a karkara ta hannun bankin duniya sannan za a tura ragowar dala miliyan 2 zuwa cibiyar bunkasa harkokin shari’a ta duniya domin fadada tsarin shari’a da yaki da cin hanci da rashawa.
Fagbemi ya kara da cewa, kwato kadarorin wata babbar nasara ce a cigaba da hadin gwiwar da ake yi tsakanin Najeriya da Amurka wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma dabbaka tsarin gaskiya da adalci.
Shi kuma a nasa jawabin, jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills ya bukaci a sanya idanu tare da sarrafa kadarorin da aka kwato ta yadda za su amfani ‘yan Najeriya.