Gaf da daliban ke shirin shiga dakunan karatunsu sai dan kunar bakin waken ya tayarda bam wanda ya hallaka dalibai da dama nan take kana ya jikata wasu.
Gwamnatin ta bada tabbacin cewa tana yin abun da duk ya kamata a gano wadanda suka shirya suka kuma aiwatar da wannan danyen aikin. Gwamnati zata tabbatar sun fuskanci shari'a domin tabbatar da matsayin gwamnati na ganin ta kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Kakakin shugaban kasa Dr Reuben Abatti shi ya fitar da sanarwar. Yace gwamnatin tayi jaje da bakin ciki akan wannan abun juyayi da ya faru da kuma bada gaskiya cewa gwamnati na daukan duk matakan da suka kamata a dauka domin tabbatar da an kawar da aukuwar irin wannan aika-aikar. Inji gwamnati, matsalar ba mai dorewa ba ce. Za'a tabbatar an kawo karshenta.
To amma bayanin gwamnatin ba wani abu sabo ba ne. Kusan duk lokacin da aka samu irin wannan aika-aika abun da gwamnati ke cewa ke nan lamarin da ya sa jama'ar kasar sun soma gajiya da kalamun gwamnati duk lokacin da aka samu asarar rayuka da hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram. Kwana kwanan nan ma dan kunar bakin wake ya kai hari akan 'yan kungiyar Shi'a lokacin da suke wani muzahara inda mutane talatin suka hallaka.
Wani mai fashin baki akan hakokin tsaron Najeriya Janaral Abdulrazak Umar mai ritaya yace irin bayanan gwamnati sun nuna cewa mutane sun fara gajiya da kalamun gwamnati. Yace na farko a ce rashin sani a bangaren gwamnati. Na biyu a ce mantuwa ko kuma kuskure. Kuma na uku ya zama sakaci ko shegantaka. Idan an yiwa mutum abu sau daya aka bashi hakuri, aka kuma yi masa na biyu aka bada hakuri to na ukun kuma fa, ai ya zama sakaci.
Janaral Umar ya cigaba da cewa abun da zai sa mutane su yadda da gwamnati shi ne idan abu ya samu mutum a tabbatar da ba zai sake faruwa ba ko dama ba'a saka ma mutum ba lokacin da na farko ya faru. A tabbatar cewa gobe ko nan gaba irin hakan ba zai faru ba. Bai kamata gwamnati ta koma tamkar wasan yara ba.
Abu mafi sauki yanzu shi ne a san inda suke. A kamasu. A hukuntasu. Illa iyaka.
Ga rahoton Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5