Jim kadan bayan harin da aka kai a makarantara sakandaren dake garin Potiskum, ‘yan kungiyar agajin Red Cross sun kai dauki a wurin.
Malam Inusa Zarma dan agajin kasa-da-kasa na kungiyar Red Cross, ya tabbatarwa Wakilin muryar Amurka Abdulwahab Mohammed cewa, dan kunar bakin wake ne ya tada bom a makarantar sakandaren kimiya dake garin Potiskum lokacin da daliban ke jiran jawabin shugaban makarantar.
A halin yanzu dai babu kowa a makarantar, duk da cewa ba a rufe makarantar ba a hukumance” inji malam Zarma. Ya kuma ce an taba kona makarantar a kwanaki baya wanda a yanzu haka ma ba a gyara wurin da ya lalace ba.
Malam Zarma yace tuni suka fara amfani da kayan agajin da kungiyar Red Cross ta kawo don kula da wadanda suka jikkata. Ya kuma kara da cewa mutane ashirin da biyu ne suka rasa rayukansu a daidai lokacin da aka yi hirar da shi, guda 46 kuma na kwance a asibiti yanzu haka.
kamar yadda za kuji a nan, ga hirar da wakilin muryar Amuka yayi da Malam Zarma.