Gwamnatin Najeriya ta dage ranar da ta ce za ta dawo da jigilar jirgin kasa na fasinja daga Abuja zuwa Kaduna sai zuwa nan da wasu “ ’yan kwanki.”
A ranar 28 ga watan nan na Nuwamba aka tsara za a maido da aikin jigilar jirgin wanda aka dakatar a watan Maris bisa dalilai na tsaro.
Ministan sufurin Najeriya, Malam Mu’azu Jaji Sambo ne ya bayyana hakan yayin wata hir da manema labarai a Abuja.
“Sufuri daga Abuja zuwa Kaduna zai fara aiki nan da wasu ‘yan kwanaki kadan.” In ji Sambo.
A cewar Ministan, sun dauki matakai na tsaro da dama a kokarin ganin an kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
“Yanzu mun saka na’urar da za mu iya ganin jirgin nan daga tashinsa har isar shi. Akwai na’urori da za sui ya gaya mana ko akwai matsala.”
A karshen makon da ya gabata ne aka yi gwajin jigilar jirgin daga Abuja zuwa Kaduna inda aka tafi da ayarin manema labarai.
Wata ma’aikaciya a tashar jirgin kasa dake unguwar Rigasa, Malama Rabi ta ce ba ta fargaba a kan za su koma bakin aiki kuma tana farin ciki da ci gaban da aka samu tare da yin addu’ar su koma bakin aiki lami lafiya.
An dai dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa daga Abuja zuwa Kaduna ne watanni takwas da suka gabata biyo bayan da ‘yan ta'adda da suka tayar da bama-bamai da suka lalata layin jirgin AK-9 a lokacin da yake kan hanyarsa ta karshe daga Abuja zuwa Kaduna a ranar
A yayin harin na watan Maris, ’yan ta’addan sun kashe mutane tara tare da yin garkuwa da fasinjoji sama da 60. An dai sako dukkan fasinjojin a lokuta dabdan-daban.
Saurari cikakken rahoton Halima AbdulRa'uf:
Your browser doesn’t support HTML5