Gwamnatin Najeriya Bata Da Ra'ayi Dangane Da Shugabancin Kungiyar Kwallon Kafar Kasar

Ministan Matasa da wasannin na Najeriya Barista Solomon Dalung, ya karyata rade radin cewar mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya tabbatar da goyon bayan shi akan shugaban kungiyar kwallon kafar Najeriya Amaju Pinnick.

Minista Dalung, ya fadi cewa ko a ranar Laraba bayan kammala taron kasa, ya zanta da mataimakin wanda ya shaida masa cewar bashi da wani zabi, dangane da wanda zai shugabanci kungiyar.

Ya kuma tabbatar da cewar wannan labarin kanzon kurege ne, inda yace dan jaridar da aka anbato ya rubuta labarin, bashi da wata alaka da kowane gidan jarida. Wanda ake zuzuta wutar cewar yana aiki da fadar gwamnati Daniel Ator, wannan wani suna ne da bashi da asali.

Ya kara jaddada cewar gwamnati bata da hannu a cikin dambarwar dake kai komo a kungiyar, duk da cewar hukumar kwallo ta duniya FIFA ta baiwa gwamnatin Najeriya wa'adi zuwa ranar 20 ga wannan watan domin su sasanta matsalar su ta cikin gida, wanda idan ba haka ba zasu cire kasar daga cikin jerin kasashe a cikin kudngiyar.