A taron ‘daurin auren ne kuma mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu, ya mayar da martani ga masu kushe yunkurin masarautarsa na samar da kudirin dokar hana masu fama da talauci a cikin al’uma auran mace fiye da ‘daya.
Babban limamin Kano farfesa Mohammad Zaharaddeen, shine ya jagoranci ‘daura auren mutane 40 daga cikin ma’aurata 1520. Yayin da limaman sauran ‘kananan hukumomin 43 suka jagoranci ‘daura auren a yankunansu daban-daban.
Gwamnatin jihar Kano ce ‘karkashin kulawar hukumar Hisba ta ‘dauki nauyin sadaki da kayan ‘dakin amare. Da yake fayyace sharuddan auren, Mallama Aminu Ibrahim Daurawa, dake zaman babban kwamandan hukumar Hisba ta Kano, yace kafin a daurawa mutanen aure an tantance lafiyarsu, an kuma umarci kowa da ya kawo shaida biyu don tabbatar da cewa suna da sana’ar yi, haka kuma duk wanda akayiwa wannan auren ba zai saki matarsa ba sai ya sanar da hukumar Hisba.
Yayin da masu zuwa da tsaki ke tofa albarkacin bakinsu dangane da yunkurin majalisar masarautar Kano na bullo da dokar hana masu fama da talauci auren mace fiye da guda.
Mai martaba sarkin Kano mallam Mahmmadu Sanusi na biyu, ya tabbatar da cewa masarautarsa tana shirya doka da zata ayyana sharuddan addinin musulunci ya tanada wanda sai mutum ya cika kafin ya ‘kara aure, kuma za a yi dokar.
Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.
Your browser doesn’t support HTML5