Wata sanarwa dauke da sa hannun Ministan Sadarwa, Rene Emmanuel Sadi, gwamnatin ta ce babu kamshin gaskiya a jita-jitar, ta kuma kara da cewa "Shugaban na cikin koshin lafiya kuma nan da ‘yan kwanaki masu zuwa zai koma Kamaru"
Ministan ya ce jita-jitar ba komai bace illa mafarkin wadanda suka kitsa ta kuma manufarsu a nan ita ce musanta hakan a hukumance.
Rahotanni sun ce shugaban na Kamaru ya rasu ne a wani asibitin sojoji da ke birnin Paris na kasar Faransa.
Paul Biya ya cika shekaru 42 da darewa kan karagar shugabancin kasar Kamaru, abin da ke nuni da cewa shi ne shugaba na biyu mafi dadewa kan karagar muki a nahiyar Afirka bayan Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na kasar Equitorial Guinea wanda ke kan karagar mulki tsawon shekaru 45.
Paul Biya mai shekaru 91 a duniya yanzu haka dai yana kan wa’adin mulkinsa karo na 7 ne a jere.