'Yan gudun hijiran da suka fito daga tarayyar Najeriya suna jibge ne a jihar Arewa Mai Nisa yayinda wadanda suka fito daga Afirka ta Tsakiya na jihar gabashin kasar.
Gwamnatin kamar yadda ta fada, zata yi anfani da kudaden ne domin samar ma 'yan gudun hijiran kayan abinci domin kada su shiga cikin wani mawuyacin hali.
'Yan gudun hijiran daga Najeriya kawai sun kai kimanin dubu dari tara ko 900,000 dake kan iyakar kasar Kamaru da Najeriya a wani wuri da ake kira dajin Miniwawo.
Mr. Michael ma'aikacin Majalisar Dinkin Duniya, ko MDD, dake aiki da 'yan gudun hijiran yana mai cewa gaskiya ne, kuma dole ne kasashen duniya suyi kokari su kawo agaji idan ba haka ba 'yan gudun hijiran zasu shiga mawuyacin hali. Ya kara da cewa kasar Kamaru ba zata iya aikin ba ita kadai. Baicin bukatar a taimakawa 'yan gudun hijiran, Mr Michael yace 'ya'yansu da iyalansu da suka baro baya su ma yakamata a taimaka masu a kuma basu ilimi mai ingianci.
'Yan gudun hijiran da suka fito daga Afirka ta Tsakiya su ma sun kai dubu dari biyu da dari shida, ko 200,600 da yanzu suke jihar gabashin kasar akan iyakokin kasashen biyu.
Kamar 'yan Najeriya Mr. Michael yace dole a taimaka masu domin yakin basasa ne ya rabasu da iyalansu. Suna bukatan samun abinci mai inganci da ilimantar da 'ya'yansu..Yace sun jajirce su tabbatar sun samu taimako.
Tun shekarar 2014 kasar Kamaru ta fara karbar 'yan gudun hijira daga tarayyar Najeriya musamman ma inda tayi iyaka da kasashen Najeriya da Chadi.
Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5