Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Kamaru Wani Mummunan Hadarin Mota Ya Hallaka Mutane 30


 Hadarin mot a Kamaru
Hadarin mot a Kamaru

Wadansu manyan motoci na daukan itacen tumba guda uku da kuma wasu safa guda biyu dake dauke da fasinjoji 35 a kowace mota suka yi mummunan hatsari a jihar gabas ta Jamhuriyar Kamaru.

Hadarin yayi sanadiyar mutuwar mutane talatin nan take kana wasu da dama suka jikata.

Malam Abdullahi magatakardan kungiyar masu sana'ar sufuri a kasar yace ya kamata gwamnati ta dauki matakan gyara hanyoyin kasar. Rashin kyawon hanyoyi yana haddasa hatsarin motoci koina a kasar.

Hadarin motoci
Hadarin motoci

Sha'aibu Gambo wani mai yawan zurgazurga a kan hanyar yace hanyar bata da kyau kuma bata da fadi sam. Wannan hadarin ba shi ne na farko ba. Injishi an taba yin wanda ya fi muni ma. Shi ma yace lokaci yayi da ya kamata gwamnati ta lura da hanyar.

Shekaru hamsin da suka gabata a fara aikin hanyar kumma kawo yanzu babu wani sabuntawa da aka yi mata duk da cewa masu bin hanyar sun karu. Baicin hakan manyan motoci masu daukan itatuwan tumba sun yi yawa saboda a yankin ake samun itatuwan

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG