Mai-magana da yawun rundunar mayakan saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet dai ya ce cikin ruwan bama-baman da mayakan saman su ka yi a yankin Yadi, dake kamar hukumar Giwa ne aka kashe Kasurgumin dan-bindiga Ali Dogo wato Yellow shi da mabiyan shi sama da talatin lokachin da su ka fake a gidan wani mai suna Alh. Gwarzo.
Shi ma kwamishinan tsaro na jahar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya tabbatar da kashe Yellown, sai dai ya ce wasu bayanan na sirri ne.
Ya ce “Rundunar tsaron suna ci gaba da gudanar da aiki na musamman kuma kwalliya na biyan kudin sabulu, amma duk da haka ba kowane bayani za a fitar ga jama’a ba,” in ji Aruwan. Ya yi kira da a kara ba wa gwamnatin goyon baya da taimako don cin nasarar wannan aiki.
Daya daga cikin shugabannin al'uma a yankin Giwa kuma tsohon Dan-majalissar dokokin jahar, Alh. Mohammadu Bawa Chocho Talban Shika, ya ce suna ganin saukin hare-haren 'yan-bindiga amma akwai gyara.
Muna kira ga jami’an tsaro da su sake dabarun su na shiga daji suna harbe harbe alhali kuwa sun san inda wadannan ‘yan ta’adda suke, in ji Bawa Chocho. Ya ce “Idan ba an kakkabe wadannan miyagu a cikin daji baki daya ba, tsugune bata kare ba.”
To ko me masana harkokin tsaro ke gani game da nasarar da jami'an tsaron ke samu kan 'yan-bindiga? Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce akwai abubuwan lura.
Ga dai sautin rahoton Isa Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5