Gwamnatin Jihar New York Na Shirin Sassaka Mutum Mutumin Ruth Ginsburg

Za a sassaka mutum mutumin Marigayiya mai shari’a ta Kotun Kolin Amurka, Ruth Bader Ginsburg a unguwar Brooklyn inda aka haifeta, abin da gwamnan jihar New York, Andrew Cuomo ya sanar kenan a ranar Asabar da ta gabata.

Ginsburg ta rasu a ranar Juma'a sakamakon matsaloli masu nasaba da wani nau’in cutar ciwon sankara ta ciki, tana da shekaru 87 a duniya.

Mai shari’ar da ke daya daga cikin mata da suka yi fice a fannin shari’a kuma ‘yar rajin kare hakkokin mata, ita ce ta zama mace ta biyu da ta shiga kotun kolin kasar a shekarar 1993.

Ruth Bader Ginsburg

Gwamna Cuomo, dan jam’iyyar Democrat, ya ce zai nada wani kwamiti don zaben mai sassaka mutum mutumin da kuma neman wurun da za a a ajiye shi.