Gwamnatin jihar dai ta gabatar da wasu bayanai ga limaman da ake bukatar limaman su fadakar da jama'a domin su samu tsira daga wannan muguwar cutar ebola da bata da magani kuma mai saurin kashe mutum.
Kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Hajiya Hadiza Abdullahi tace bukatun sun hada da yin tsafta da kuma yin taka tsantsan da cin naman daji da kuma takaita yin zirga zirga da gawa daga wannan gari zuwa wancan.
Kwamishaniyar tace matakan da gwamnati ta dauka sun hada da hana daukar gawa daga wata jiha zuwa wata har ma gwamnatin tarayya na son a hana ma tsakanin kananan hukumomi. Tace mutane suyi hakuri da matakan da gwamnati ta dauka domin idan nan da wata uku an shawo kan cutar sai a daina. Tace gwamnati tana tsoron yaduwar cutar matuka.
Limaman sun ce bayanan da aka yi masu basu sabawa musulunci ba. Sakataren majalisar limaman Imam Umar Faruk yace an yi masu bayani daki-daki game da illar cutar. Sun kuma gamsu da duk bayanan. Duk matakan kariya da za'a dauka an bayyana masu kuma basu sabawa musulunci ba. Sun amince da abun da suka fada masu kuma zasu fadakar da jama'a game da illar cutar domin su kiyaye.
Limaman sun ce daga yau zasu fara fadakar da jama'a a cikin hudubobin da zasu gudanar a masallatai. Dr Salawudeen Suleiman daya daga cikin limaman yace yanzu da ak fadakar dasu zasu hadu da jama'arsu.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5