Majalisar dai tayi wani zama ne na musammam a jiya Alhamis, inda mataimakin shugaban majalisar Hon Husaini Ibrahim Agaye, ya bankado wannan batu. A baya dai akwai makurden kudaden da sabuwar gwamnatin tace tsaffin jami’an gwamnatin sunyi awon gaba da su, amma har ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayani kan maganar.
Daya daga cikin yan majalisar Hon Malik Madaki Boso, yace a yau kimanin watanni takwas da rantsar da wannan gwamnati, amma har yanzu batayi komai kan wannan batu ba, duk da yake in aka duba daga gwamnatin tarayya zuwa sauran jihohi kowa na bin diddigin duk wanda suka saci kudi ana karbowa, sai ga shi gwamnatin Neja tayi shiru.
Sai dai majalisar ta bayyana matsayinta na ganin an hukunta duk wanda aka samu da laifin wawure kudaden jama’a a baya.
Gwamnatin jihar dai ta mayar da martani kan wannan matsayi na yan majalisar, ta hanyar sakataren yada labarun gwamnan jihar Neja, Jibrin Baba, inda yace baki daya daga yan majalisar zuwa mutanen jihar zasu ga mamaki kan wannan maganar, ya kuma ce ana nan ana bincike har an kirawo wasu sun bayar da bayanai amma bai ambaci sunan kowa ba.
Masu nazarin al’amura na ganin cewa da wuya binciken yayi wani tasiri, musammam yadda ganin irin dangantakar da take tsakanin tsohon gwamna Babangida Aliyu, da kuma gwamnan na yanzu Alhaji Abubakar Sani Bello.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5