A firar da Muryar Amurka tayi da Arch. Ahmed Abdullahi Kabiru babban daraktan hukumar dake kula da harkokin ruwa da muhalli ta jihar, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatin ta dauki wannan matakin.
Yace yawan tallace-tallace da ake yi akan tituna babban kalubale ne ga harkar sufuri a jihar, musamman ma a birnin Legas. Yayinda motoci ke tafiya mutane sai su kawo kayayyaki akan tituna suna bin motoci domin su sayar da kayansu ko su bazasu gefen hanya. Tamkar babu abun da basa kawowa kan hanya sayarwa. Hakan yana sanadiyar hadarin mota, wani zubin ma har a rasa rai ko rayuka.
Wata matsala kuma ita ce ta rashin tsafta. Bayan an share birnin kakaf sai wadan nan masu tallace-tallace su yi kaca-kaca da wuraren da aka share da shara. Birnin sai ya koma kamar ba'a shareshi ba.
Akan wai tsaurara dokar zata fitar da wasu, musamman matasa, daga samun abun da zasu ci su kuma biya bukatunsu na yau da kullum, Abdullahi Kabiru yace suna yi ne domin ganin dama. Akwai kasuwanni da dama amma sai a ga babu kowa ciki domin duk sun bazu kan tituna suna talla. Sun bar kasuwannin fanko sun dawo kan hanya sun baza kolinsu. Yace yin hakan ba daidai ba ne domin ana samun hadarurruka, masu tallan suna jin ciwo ko ma su mutu gaba daya domin motoci sun bugesu. Yace ba za'a cigaba da rayuwa haka ba. Dole a kawo gyara.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5