Sai dai masana sun ce walwalar al’amarrorin shi ne babban abin da gwamnatin ya kamata ta fara baiwa fifiko.
A bara ne gwamnatin Kanon ta bullo da jadawalin gudanar da garanbawul ga tsarin karatun tsangayu, bayan da ta kaddamar da shirinta na Ilimi Kyauta kuma wanda yake dole daga matakin fraimare zuwa Sankandare a fadin jihar.
Shekara guda da kaddamar da garanbawul din ga makarantun tsangayun, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi bitar nasarori da-ma kalubale.
Ya ce tsangaya magana ce ta almajirai, kuma sun dauki matakai so sai, kuma an bude makarantu manya, da kayan makaranta kuma za a koya masu karatun zamanida na islama.
Sai dai Comrade Yahaya Shu’aibu Ungogo dake sharhi kan lamuran ilimi yace, al’amarorin dake koyar da almajiran ya fi dacewa fara baiwa kulawa.
Ya ce su ne wadanda ya kamata afara kyautata masu kuma duk gaba daya jihohi su hada kai don samun nasara ba wai a Kano kawai ba
Amma masu bincike a wannan fanni na ilimin tsangayu sunyi tsokaci akan yawan alkaluman makarantun tsangayu da daliban su a Kano da-ma yankin arewacin Najeriya.
A saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5