Gwamnatin Jihar Kaduna Zata Samar Da Cibiyoyin Horar Da Kangararru

Bayan wata ziyarar bazata da mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hajiya Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe, ta kai wata cibiyar horar da kangararru, da matasa masu shaye-shaye. Ta bayyana cewar suna cikin mawuyacin hali, kana da yawa da ga cikin su suna fama da rashin lafiya da suke bukatar taimakon gaggawa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jjhar Kaduna Mr. Samuel Aruwan, yayi karin haske akan irin halin damuwar da suka sami matasan ciki, wanda suka hada da kananan yara. Kwamishinan yace sun samu rahoton sirri daga wasu masu kishin al’ummah, wanda suka yi bincike suka tabbatar da hakan kafin suka dauki matakan da sukakai ga ganin halin da suke ciki.

Cibiyar dake anguwar ‘Limanci Kona’ a cikin birnin Zariya, sun same su cikin halin damuwa, kuma gwamnati ta dauki nauyin kyautata rayuwar su, wanda yanzu haka suke hannun hukumomi kuma ana kula da lafiyar su yadda ya kamata.

Ya kuma kara da cewar gwamnati zata dauki kwararan matakai wajen ladabtar da duk wadanda aka samu da aikata laifukan cin zarafin ‘bil adama. Kana yanzu haka gwamnatin na shirin dawo da tsarin cibiyoyin kangararru mallakar gwamnatin jiha, karkashin jagorancin ma’aikatar jin dadi da walwalar jama’a.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Kaduna Zata Samar Da Cibiyoyin Horar Da Kangararru