Rufe wadannan makarantu ya biyo bayan jerin hare-hare ne daga mahara dauke da makamai a kan makarantu wadanda hukumomi suka ce suna yin barazanar lalata tarbiya da ilimin yaran Najeriya har abada.
Jami’an Hukumar Kula da Ingancin Makarantu na Jihar Kaduna sun ce binciken da aka yi game da hatsarin ya nuna makarantun 13 su ne suka fi fuskantar hadari.
Harin da aka kai makarantar sakandaren Betel ranar Litinin shi ne na baya-bayan nan a yawan sace-sacen makarantun domin neman kudin fansa kuma shi ne na hudu na irin wannan sata da aka yi a jihar cikin watanni biyar.
Mahukunta a Kaduna sun ce an ceto mutane 26, ciki har da wata malama mace, kuma sojoji suna cikin neman sauran wadanda aka sace.
Seun Bakare na kungiyar ta Amnesty International ya ce hare-hare da rufe makarantu na nuna mummunar barazana ga ilimi a Najeriya.
Jami'an Najeriya na kokarin gano 'yan bindigan na garkuwan da aka yi wa malaman makaranta, kwana guda bayan yunkurin sace daliban.
Karin bayani akan: Bethel Baptist High, Boko Haram, Amnesty International, Kaduna, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Bakare ya ce "Abin kunya ne kwarai da gaske cewa a wani bangare, 'yan fashi da' yan Boko Haram suna kai hari ga yara da kuma hakkinsu na neman ilimi, a daya bangaren kuma, matakin da gwamnati ta dauka shi ne na rufe makarantu. Abin da gwamnati ta yi shi ma hari ne ga ilimi kuma wannan kwata-kwata bai yi ba "
Yawan sace-sacen mutane na baya-bayan nan na ci gaba da ta’azzara matsalar ilimi a arewacin Najeriya, yankin da aka san shi da karancin matakan ilimi, da kuma sama da kashi 70 cikin 100 na wadanda suka fice daga makarantun Najeriya.
Duk da alkawarin da gwamnati ta yi na tabbatar da tsaron makarantun, masu suka sun ce ko dai ba ta so ko kuma ta gaza iya magance matsalar.
Iyayen Daliban Da Aka Sace A Najeriya, Aun Gudanar Da Addu’o’i
Your browser doesn’t support HTML5