Gwamnatin Jihar Kaduna na Son Raba Dusa da Hatsi

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.

Jama’a assalamu alaikum, A ci gaba da tantance ma’aikata da Gwamnatin jihar Kaduna take gudanar ana samun korafe korafe dagane da wannan aiki.

Aikin tantance ma’aikatan dai zai dauki dan lokaci amma yana fama da cunkoson layi, yayin da wasu ke korafin cewa sai layi yazo kansu a tashi ace su dawo kuma koda an dawo bazasu samu ba .

Wasu daga cikin ma’aikatan da suka sakaya sunan sun ce tantancewar na fama da cikas domin sun kai mako daya suna halartar wajen da ake gudanar da aikin tantancewar amma har yanzu hakar bata cimma ruwa ba.

Samuel Samaila Aruwan mai taimakawa Gwamnan jihar Kaduna kan kafofin yada labarai ya bayana dalilin gudanar da tantance ma’aikatan da cewa gwamnati ta naso ta raba dusa da hatsi ne domin sanin gaskiyar adadin ma’aikatan jihar a matakin jihar da kuma na kananan hukumomi.