Gwamnan ya bayyana hakan ne lakocin da ake gabatar masa da wasu 'yan mata guda ashirin da gwamnatin zata tura zuwa kasar Sudan domin su koyo aikin likitanci.
Wannan shi ne karo na biyu da jihar zata tura irin wadannan dalibai mata da nufin koyo aikin likitanci a kasar ta Sudan. Gwamnan yace babu abun da mutum zai iya yi domin barin baya idan ba baiwa al'umma ilimi mai anfani ba.
Bayan gabatar da daliban da kuma basu kyautar kwamputoci da mika masu wasikunsu na basu damar zuwa koyon aikin likitanci a Sudan sai wakilin Muryar Amurka ya tambayeshi ko menene ya bashi karfin gwiwar daukar matakin da ya dauka. Gwamnan yace babban abu shi ne "muna bukatar 'ya'yanmu mata su koyi aikin likita domin akwai wasu ayyukan da ake bukatarsu suyi". Wadannan ayyukan sun hada da kiwon lafiyar yara da kula da mata masu juna biyu har zuwa lokacin da zasu haihu.
Gwamnan ya kara da cewa kowace shekara zasu aika da dalibai hamsin zuwa kasar ta Sudan kana su tura 'yan mata dari cikin jami'o'in dake kasar ta Najeriya. Zasu cigaba da shirin nan da zuwa shekaru biyar. Kodayake nan da shekara biyar baya kan mulki amma dole a dauki matakin magance karancin likitoci a jihar.
Akan ko nawa ne gwamnatin zata kashe gwamnan yace a manta da batun kudi. Karatu ba abun da za'a lissafa da kudi ba ne. Yace ko zasu kashe miliyan dari biyu akan kowace daliba basu damu ba.
Babban sakatare a ma'aikatar ilimi Alhaji Lawal Maina Mahmud yace a yanzu haka gwamnati ta kashe fiye da nera miliyan sittin da biyar domin daukan nauyin daliban. Har yanzu suna kan zakulo wasu daliban domin basu damar cigaba da karatun aikin likita.
Daliban da aka zanta dasu sun yi murna da mika godiyarsu ga Allah da gwamnatin jihar.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5