Gwamnatin Jihar Borno Zata Cigaba da Biyan Kudaden Jarabawar Daliban Sakandare

Gwamnan Borno Kashim Shettima

Duk 'yan makarantun sakandaren Borno da aka dakatar dasu cikin shekaru biyun da suka gabata gwamnatin jihar zata cigaba da biyan kudaden jarabawarsu ta kammala karatun sakandare

Idan ba'a manta ba an rufe duk makarantun sakandaren Borno har na tsawon shekaru biyu biyo bayan sace 'yan matan Chibok daga makarantarsu da 'yan Boko Haram suka yi, kuma har yanzu akwai wasu da dama a hannun 'yan ta'adan.

Gwamnatin jihar ta bada sanarwar cigaba da biyan kudaden jarabawan daliban lokacin da wani jami'in gwamnatin ya ziyarci wasu makarantun da aka sake budewa a cikin birnin Maiduguri. Yace za'a yi masu wani gwaji kuma sai wanda ya ci gwajin za'a bari ya rubuta jarabawar karshe.

Kwamishanan ilimi na jihar Borno

Yace gwamnan jihar ya riga ya basu umurni akan cewa za'a cigaba da biyan kudin jarabawa na NECO da WAEC amma sai an tantancesu da wani gwaji. Wadanda suke bukatar a basu lokaci za'a basu. Wadanda suka kuma shirya su yi jarabawar karshe zasu yi.

Daliban da lamarin ya shafa sun yi murna da fatan Allah ya ba gwamnan ikon cika alkawarin biyan kudaden na jarabawarsu.

Amma duk da wannan alkawarin da gwamnatin ta yiwa daliban malamansu na kokawa da rashin biyansu albashinsu. Wasunsu sunce sun kwashe fiye da watanni hudu ba'a biyasu ba sakamakon tantance ma'aikata da gwamnatin tace tana yi..

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Borno Zata Cigaba da Biyan Kudaden Jarabawar Daliban Sakandare - 3' 43"