Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kori Gidan Talibijan Na AIT daga Harabarsa

GWAMNAN JIHAR BAUCHI BARRISTER M.A. ABUBAKAR

A wani yunkuri dake da alaka da manufar siyasa, gwamnatin jihar Bauchi ta ba gidan talibijan na AIT ya kwashe kayansa ya bar inda yake yanzu a cikin birnin Bauchi nan da makonni biyu

Air Commodor Ahmed Baba Tijjani mai ritaya babban mai tallafawa gwamnan Bauchi akan ayyuka na musamman shi ya bada sanarwar da ta tada gidan talibijan din na AIT.

Ya bada dalilan da suka sa gwamnatin ta dauki matakin korar gidan talibijan din daga harabarsa. Yace wai gwamnatin jihar Bauchi na bukatar wurin domin bunkasa kafofin yada labarunta.

Da Muryar Amurka ta fadawa jami'in gwamnatin Bauchi cewa gwamnatin bata jin dadin abubuwan da gidan radiyon da talibijan na AIT ke yayatawa shi ya sa gwamnati take neman tadasu, sai yace ba haka ba ne. Yace ba siyasa ba ce bukata ce ta taso.

A nasu ba'asin babban jami'in gabatar da shirye shirye na AIT Murtala Tanimu Lere yace ba'a tada mutum wurin da yake ba tare da biyansa hakkokinsa ba. Yace sun zuba dukiyarsu a wurin kuma gwamna mai iko wanda ya yi shekaru takwas yana mulkin jihar ya basu. Yace suna da takardun mallakar wurin. Saboda haka ba za'a tashesu ba sai an biyasu diya kamar yadda doka ta tanada.

Idan an biyasu sai su nemi wani wuri su koma su rabu da gori. Yace babu yadda zasu cigaba da aikin jarida da bada labarin gwamna da mataimakinsa da kakakin majalisa kawai. Idan sun yi hakan kada ma su yi tsanmacin al'umma zasu sauraresu.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kori Gidan Talibijan Na AIT daga Harabarsa - 3' 00"