Masu sace mutane suna yin hakan ne domin neman kudin fansa, idan kuma sun sace dabbobi su sayar su samu kudi, lamarin da ya zama tamkar wata sana'a.
Yawan sace sacen mutane ya sa wani dan majalisar dattawa dake wakiltar Bauchi ta tsakiya ya fadawa jaridar Daily Trust cewa 'yan Boko Haram sun kafa sabbin sansanoni a jihar.
Amma mai ba gwamnan Bauchi shawara akan harkokin tsaro Bigediya Ladan Yusuf mai ritaya ya musanta abun da shi dan majalisar dattawan, Isa Haman Misau, ya fada tare da yin bayani.
Birgediya Janar Yususf yace babu batun Boko Haram kamar yadda Isa Haman Misau ya fada, illa masu satar mutane domin neman kudin fansa. Yace sun samu nasarar cafke wasu gagga daga cikinsu.
Yace jama'a basu sani ba cewa ana jibge sojoji a wurare daban daban a jihar kuma idan mutane sun gansu sai su kama gudu suna tsamnanin 'yan Boko Haram ne.
Sun fadakar da mutane idan sun ga mutane su bugo waya domin a tabbatar masu ko wadanne irin mutane ne.
Birgediya Ladan Yusuf ya kara jaddada cewa babu Boko Haram a jihar. Yace ko ranar Asabar an kama mutane goma sha daya. Ranar Alhamis an kama mutane biyu wadanda aka sansu sosai da aikata mugun hali.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.