Gwamnatin jihar Arizona dake Amurka, ta bada sanarwar cewa zata daukaka kara a hukuncin da kotun tarayya ta yanke na hana aiki da wasu muhimman bangarorin dokar dakile ‘yancin bakin hauren da basu da takardun izinin shiga Amurka, a dai dai lokacin da dubban mutane ke ci gaba da zanga-zangar nuna rashin amincewa da aiki da dokar da ta fara aiki a Arizona tun daga jiya Alhamis. Lauyoyin dake baiwa Gwamnar jihar Arizona Jan Brewer kariya, sun shigar da daukaka kararsu a babar kotun daukaka kara dake San Francisco, California. Lauyoyin sun kuma bukaci kotun daukaka karar ta gaggauta yanke hukunci.Yayin da ake wannan, ’yan sanda a Phoenix sun kama mutane sama da talatin saboda toshe titunan da ake bi a zanga-zangar da suka shirya a wajen ofishin shugaban ‘yan sanda jiya Alhamis.Gwamnatin jihar Arizona dake Amurka, ta bada sanarwar cewa zata daukaka kara a hukuncin da kotun tarayya ta yanke na hana aiki da wasu muhimman bangarorin dokar dakile ‘yancin bakin hauren da basu da takardun izinin shiga Amurka, a dai dai lokacin da dubban mutane ke ci gaba da zanga-zangar nuna rashin amincewa da aiki da dokar da ta fara aiki a Arizona tun daga jiya Alhamis. Lauyoyin dake baiwa Gwamnar jihar Arizona Jan Brewer kariya, sun shigar da daukaka kararsu a babar kotun daukaka kara dake San Francisco, California. Lauyoyin sun kuma bukaci kotun daukaka karar ta gaggauta yanke hukunci.Yayin da ake wannan, ’yan sanda a Phoenix sun kama mutane sama da talatin saboda toshe titunan da ake bi a zanga-zangar da suka shirya a wajen ofishin shugaban ‘yan sanda jiya Alhamis.
Gwamnatin jihar Arizona dake Amurka tace zata daukaka kara a kan hukuncin kotun tarayya dangane da dokar da zata bada damar dakile ‘yancin bakin haure
Gwamnatin jihar Arizona dake Amurka, ta bada sanarwar cewa zata daukaka kara a hukuncin da kotun tarayya ta yanke na hana aiki da wasu muhimman bangarorin dokar dakile ‘yancin bakin hauren.