Malaman Addinin Islama da ke garin Dakar, babban birnin kasar Senegal sun yi kira ga mazauna birnin da kewaye da kada su biya kudin wuta saboda sun yi wata da watanni su na fama da zama cikin duhu, ba wutar lantarki.
Imam Youssoufa Sarr ya fada a ranar Alhamis cewa kin biyan kudin wutar wani mataki ne su ka dauka da niyyar yin matsin lamba ga kamfanin wutar kasar mallakin gwamnati ya gyara wannan matsala da jima tana addabar mutanen birnin Dakar da kewaye.
Ya ce gungun Malaman Addinin Islamar za su sake waiwayen al’amarin ranar 17 ga watan gobe na Agusta, kuma ya ce za su kawo karshen matakin kin biyan kudin wutar idan sun ga kyautatuwar samun wutar lantarki.
Ko da yaushe a lokacin zafi ana fama da dauke wuta a kasar Senegal, lokacin da ake samun karuwar bukatun shan ruwan sanyi da sanyaya gidaje. Amma matsalar dauke wutar bana ita ce mafi muni a kasar a ‘yan shekarun nan. Yawan dauke wutar ya janyo yin manya-manyan zanga-zanga a cikin birnin Dakar da kewaye.
Gwamnatin kasar ta dora laifin dauke wutar akan matsalar rashin ingancin makamashin da ake yin amfani da shi a cikin injunan cibiyar sarrafa wutar lantarkin. Ministan makamashin kasar Senegal Samuel Sarr ya fito bainar jama’a ya roki al’ummar kasar gafara, sannan kuma ya yi alkawarin cewa kafin ranar 15 ga watan gobe na Agusta za a koma ga samun wutar lantarki da kyau kamar da.