A jiya Laraba ne wasu rahotanni suka karade kafafen sada zumunta har ma da wasu kafafen yada labarai, da ke bayyana dawowar kungiyar banga ta Bakassi Boys a yankin kudu maso gabashin Najeriya, da sunan taimakawa wajen yaki da hare-haren ‘yan bindiga da satar mutane a yankin.
To sai dai kuma wata sanarwa da kwamishinan watsa labarai na jihar Anambra Don Adinuba ya fitar, ta bayyana wadannan rahotannin a zaman “kanzon kurege” da ba su da tushe balle makama.
Sanarwar ta ce “wani ne kawai da ba’a gane ko waye ba, ya watsa wani hoton bidiyo, yana ikirarin cewa kungiyar ta tsagera mai cike da cece-kuce ta dawo, inda kuma nan take hoton bidiyon ya karade ko ina, ba tare da tantance gaskiyar lamari ba.”
“Gwamnatin jihar Anambra ta na tabbatarwa jama’a cewa babu kungiyar ‘Bakassi Boys’ a cikin jihar, kuma ba za’a kuma yin amfani da ita ba a cikin jihar,” sanarwar ta ci gaba da cewa, “jihar Anambra jiha ce da ke zaune lafiya, duk kuwa da kalubalen tsaro da yankin ke fuskantar a ‘yan watannin nan.”
To amma kuma sanarwar ta bayyana wani kokari da al’ummar Awka suke yi na bankado wani gungun ‘yan kungiyar matsafa da suka addabi jihar sakamakon rashin isassun jami’an tsaro a yankin, wanda ta ce wasu ‘yan jarida da kafafen yada labarai suka yi wa mummunar fahimta, suka kuma fassara shi a zaman dawowar kungiyar ta ‘Bakassi Boys’.
Ta ce kungiyoyin matsafan suna fada da junansu, wanda yayi sanadiyyar mutuwa da raunata jama’a da dama. “Hakan ya sa matasan Awka da suke cikin damuwa da tabarbarewar tsaro a yankin su, suka dauki matakin farautar ‘yan kungiyar asirin daga maboyarsu.”
Akan haka sanarwar ta bukaci jama’ar jihar da su yi watsi da wannan labarin da kuma bidiyon da ake watsawa, kana kuma su ci gaba da gudanar da al’amuransu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.
A can baya dai an yi amfani da kungiyar bangar ta ‘Bakassi Boys’ a jihohin Abia da Anambra, sa’adda jihohin biyu da ke makwabtaka da juna suke fuskantar yawaitar ayukan ‘yan ta’adda.
To sai dai ayukan kungiyar da ta soma rikidewa ta ‘yan tsagera sun haifar da cece-kuce, lamarin da ya sa aka soke kungiyar baki daya a lokacin.