Gwamnatin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo Ta Hana Masu Rajin Kare Hakkin Bil'adama Aiki

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ta hana wata mai bincike kan keta hakkin bil Adama ci gaba da gudanar da bincikenta a kasar, hakan yasa kungiyoyin kare hakkin bil Adama ke cewa “wannan shine yunkurin koma baya ga rahotannin cin zarafin dan Adam, a wannnan lokacin da ake ‘kara samun muzgunawa daga gwamnatin kasar.”

A jiya Talata ne kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Right Watch, tace gwamnatin jamhuriyar dimokaradiyar Congo ta soke izinin da aka baiwa Ida Sawyer, wata mai bincike, bayan da ta sabunta izinin bincikenta a kasar cikin watan Mayun shekara ta 2016. Sawyer dai ta dade tana yin aikin ta a kasar tun shekara ta 2008.

Kungiyar Human Right Watch tace haka kurum jami’an kula da shige da ficen baki suka ce an dakatar da sabon izinin bincikenta, a lokacin da zata yi tafiya daga babban filin saukar jiragen sama na Kinshasa. Kungiyar tace Sawyer ta cike takardun sake samun izinin bincike a kasar, amma aka hanata ranar Litinin din da ta gabata, aka kuma bukaci ta bar kasar cikin kwanaki biyu.

Human Right Watch dai tace babu wani dalili da aka bata na rashin bata wannan izini, kuma tace mai binciken wadda ke bin diddigin cin zarafin bil Adama, za ta yi amfani da abin da aka fada mata ta bar kasar.

2.