Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Masu Zanga Zangar Kin Jinin Gwamnati A Habasha


Habasha
Habasha

Mutane da yawa ne suka mutu kana wasu da dama suka samu rauni iri daban-daban , lokacin da jami'an tsaron kasar Habasha suka budewa wasu masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati wuta a cikin karshen satin data gabata.

Kamar yadda jamiyyar adawa ta ruwaito ita da kungiyar kare hakkin bil adama.

Kungiyar Amnesty International tace a kalla mutane 97 suka mutu lokacin da suke gudanar da wannan zanga-zangar a yankin gundumar Oromia dake yankin na Amhara.

A Oromia, wasu jamiaan biyu dake cikin jamiyyar Oromo Federalist Congress sunce mutane sama da 30 ne aka kashe a ranar asabar da lahadi.

Mataimakin shugaban jamiyyar Mulatu Gemuchu ya shaidawa muryar Amurka cewa, wadannan mutanen da suka mutu sun bazu ne zuwa birane 12 dake fadin kasar.

Daya daga cikin biranen da wannan abu yafi shafa ko shine Bahir Dar, dake yankin babban birni Amhara.

Wannan yasa tilas jamiyyar adawa ta Semayawi dakatar da taron ta data shirya zata gudanar, tace dalilin ko shine rashin amincewa da gwamnbati bata yi na ganin ta gudanar da wannan taron data yi aniyar yi.

Sai kuma ana sa ran masu zanga-zanga su taru a ranar lahadi domin nuna goyon bayan su ga masu zanga-zangar kana su nemi damar ganin an tattauna batutuwan kananan hukumomi .Shedun gani da ido dai sun tabbatar wa muryar Amurka cewa jamiaan tsaro sun halbi mutane cikin taro haka nan zikau. Kungiyar Amnesty tace nan take mutane 30 suka riga mu gidan gaskiya.

Sai dai mai Magana da yawun yankin gundumar gwamnatin Amhara, Negussu Tilahun yace mutane 7, don haka gwamnati ce keda alhakin kare kasar tare da ganin anbi doka sau da kafa

XS
SM
MD
LG