Bayan sama da mako daya na zanga zanga da ya gurgunta harkoki a wasu sassan Hong kong, shugabannin dalibai sun yarda zasu tattauna da jami’an gwamnati domin shimfida sharuddan tattauna kan bukatarsu na ganin an aiwatar da sauye sauyen a harkokin siyasar yankin.
An sami wannan ci gaban ne saboda lafawar da aka samu daga zazzafar zanga zangar da ake yi a jiya litinin,wanda ya baiwa ma’aikatan gwamnati damar komawa bakin aiki.
Lester Shum na babbar kungiyar dalibai a Hong kong, ya gabatar da sharuddan da za a bi a duk shawarwarin da za a yi nan gaba tsakanin masu zanga zanga da jami’an gwamnati, lokacinda suka zauna jiya litinin.
Daya daga cikin sharuddan da sassan biyu suka amince da shi, shine cewa, wajibi ne akan gwamnatin yankin, ta aiwatar da duk wata yarjejeniyar da aka kulla a tattaunawar da aka yi.
Daya yake magana jiya litinin, babban jami’in harkokin mulki na Hong Kong Leung Chun-ying, yace, “da gaske gwamnati take yi dangane da shawarwari da masu zanga zanga kan sauye sauye a tsarin mulkin yankin”, wadanda suke bukatar kada hukumomin Beijing su tantance ‘yan takara daga yankin wadanda zasu tsaya zabe.