Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Rajin Demokuradiyya A Hong Kong Suna Ci Gaba Da Zanga Zanga


Dandazon masu zanga zanga a Hong Kong.
Dandazon masu zanga zanga a Hong Kong.

A Hong Kong masu zanga zanga da suka kafa sansanoni a rana ta biyar suna barzanar zasu fadada tada kayar bayar da suke idan shugaban yankin Leung Chun-ying bai biya musu bukatunsu ban a aiwatar da sauye sauyen ta fuskar demokuradiyya.

A cikin wata ‘yar gajeruwar sanarwa da ‘yan kaka-gida a sansanonin kasuwancin yankin suke yi, sun ce zasu bada sanarwar mataki na gaba da zasu dauka muddin shugaban yankin bai biya musu bukatunsu ba, da suka hada da ganin yayi murabus.

Leung bai nuna wata alamar cewa zaiyi murabus ba. A cikin wani jawabi da yayi talatan nan, Mr. Leung yayi kira ga masu zanga zangar “su cika alkawari da suka yiwa yankin da jama’arta” su daina zanga zangar ba tareda wani bata lokaci ba, al’amari da yace ya wuce makadi da rawa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG