Al'umman yankin Bawku na jahar maso gabashin kasar sun nuna damuwarsu matuka bisa matakin da gwamnati ta dauka na rufe gidajen rediyon da suka hada da Gumah FM, Bawku FM da Souce FM tare da Zahra FM, inda suke cewa, hakan zai hana su samun labarai tare da wasu abubuwan da zasu amfanar da su cikin harkokinsu na yau da kullum.
A wani jawabin da darektar sashen kula da harkokin kamfanoni a hukumar sadarwa ta kasa NCA, Nana Defie Badu ta gabatar bisa matakin rufe gidajen rediyo, tace;
"hukumar tsaro ta kasa ta National Security bayan bincike mai zurfin gaske da ta aiwatar, ta tabbatar da cewa, wadannan gidajen rediyo suna bada gudunmuwa wajen kawo rashin zaman lafiya a yankin Bawku don haka ta dauki wannan mataki da doka ta bata damar ladabtar da masu yada labarai har in suka aikata ba daidai ba. Muna aiki tare da hukumar tsaro ta kasa ne domin ganin an samu zaman lafiya a yankin"
An yi hatsarar rayuka masu yawa da dukiyoyi kazalika dubban jama'ar yankin sun yi kaura da ga Bawku zuwa kudancin kasar domin neman mafaka.
Gidajen rediyo hudun sun nuna rashin jin dadinsu bisa wannan mataki.
A hirarsa da muryar Amurka, Nurudeen Gumah darektan gidan rediyo ta Gumah FM ya ce;
"kafin hukumar NCA ta rufe gidajen rediyo ya kamata ta rubuta mana wasika ta nuna mana dalilin hakan tare da baiwa gidajen rediyo wa'adi yaso mu shirya in kuma muna da wani jawabi ne mu gabatar amma kai tsaye wasu dakarun soja suka iso a gidajen rediyon tare da rufe su da kuma yin awon gaba da naurorin transmitter dinsu. Babu wanda ya tuntubi mu kuma babu wanda ya bamu takarda cewa ga matakin da za'a dauka a kanmu, nan take aka kawo takarda kuma rufe gidajen ya biyo baya".
A bayaninsa, Umar Sanda Ahmad daya daga cikin masu sharhi kan sha'anin tsaro a Ghana yace wannan mataki ya dace sosai sabida har in an shirye shiryen da tashoshin suke gabatarwa na bada gudunmuwa wajen rura wutar rikici a yankin dole ne hukumomi su hana hakan. Umar Sanda ya bada misali da abinda ya haifar da rikicin kabilanci a kasar Rwanda bayan wasu kalaman tunzura jama'a da aka gabatar a rediyo inda hakan zai iya faruwa adon haka matakin gwamnati yayi daidai.
Rediyo na daya daga cikin abubuwan da ke bada gudunmuwa wajen karfafa demokardiyya amma kuwa har in zai janyo rikici to rufeshi shine mafi alkhairi saboda demokradiyya baya huru wutan rikici inji Shariff Abdul Salam mai sharhi kan al'amurran yau da kullum.
Kafin rufe wadannan gidajen rediyo guda hudu, Majalisar wanzar da zaman lafiya ta kasa ta bukaci gwamnati ta rufe biyu daga cikin gidajen rediyo hudu da aka rufe, wato Bawku FM da Souce FM bisa gudunmuwar da tace suke bayarwa wajen hassa wuta rikicin kabilanci a yankin.
Gwamnatin Ghana ta sha rufe gidajen rediyon saboda rashin sabunta lasisi amma ba saboda matsalar tsaron kasa ba kamar matakin da ta dauka kan wadannan gidajen rediyo hudu da ke yankin Bawku.
Tuni dai gidajen rediyon suka mika takardar bukatarsu ga gwamnati domin ganin an samu nasarar watsa shirye-shiryen da ake bukata maimakon rufe gidajen rediyon.
Saurari rahoton Hamza Adam:
Your browser doesn’t support HTML5