Gwamnatin Filato Ta Yi Kashedi Ga Masu Shirin Yin Zanga-zanga

Gwamna Simon Lalong (Facebook/PLSG)

A ‘yan kwanakin da suka gabata Jos, babban birnin jihar da kewayensa, ya tsunduma cikin rikici lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.

Hukumomi a jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya, sun yi gargadi ga wadanda suke shirin gudanar da zanga-zanga a ranar Talata 7 ga watan nan na Satumba.

“Labari ya zo wa gwamnatin jihar Filato cewa, akwai rade-radin da ake yi na cewa an shirya wata zanga-zangar daga Talata 7 ga watan Satumbar 2021.” Wata sanarwa dauke da sa hannun Kwamishinan yada labarai Dan Manjang ta ce.

“Duk da cewa gwamnatin na sane da ‘yancin da doka ta ba ‘yan kasa na damar yin zanga-zangar lumana, muna masu tunatawar jama’a cewa, dokar da ta haramta duk wani irin gangami nan na aiki, musamman a daidai wannan lokaci da jihar ke kokarin farfadowa daga hare-haren da suka faru a kwanan nan, wadanda suka shafi wasu sassan jihar.”

A ‘yan kwanakin da suka gabata Jos, babban birnin jihar da kewayensa, ya tsunduma cikin rikici lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dumbin dukiyoyi.

Har yanzu garin na Jos na karkashin dokar hana fita daga 6 na safe zuwa shida na yamma.

“Saboda haka, gwamnati na gargadi ga wadanda suka shirya wannan zanga-zanga da su janye ta saboda zaman lafiya. An sa jami’an tsaro su zauna cikin shirin ko ta kwana tare da ba su umarnin su kama duk wanda ya take wannan doka.”

Hukumomin jihar ta Filato har ila yau, sun yi kira ga al’umar jihar, da su fita harkokinsu na yau da kullum ba tare da wani fargaba ba, tana mai kuma kira ga iyaye da su ja kunnen ‘ya’yansu.