Gwamnatin Jihar Filato Ta Samar Da Dandamalin Inganta Tsaro

Gwamnan Jihar Filato Barrister Simon Bako Lalong

Tare da taimakon Majalisar Dinkin Duniya jihar Filato ta samu wani dandamalin tattaro bayanai akan halin tsaro a koina a cikin jihar da zai taimaki jami’an tsaro daukan matakan gaggawa domin dakile duk wani aukuwar tashin hankali

Gwamnatin jihar Filato ta ce ta samar da motoci da wata dandamali da zasu taimaka wajen samar da bayanan tsaro da gaggauta kai doki a duk inda aka samu matsalar tsaro a duk fadin jihar.

Gwamnan jihar Simon Bako Lalong shi ya kaddamar da dandamalin a hedkwatar tsaron farin kaya dake jihar mai lakabin Operation Rainbow.

Gwamna Lalong yace daukan wannan mataki ya zama dole saboda matsalolin tsaro da a ke samu jifa-jifa a wasu sassan jihar. Yace sun rabawa sojoji da jami’an tsaro, da kuma ‘yan sanda gaba da suke jihar Filato, motoci. An sa masu komai a jikin motocin da zasu dinga nuna duk inda ake tashin hankali a jihar”.

Gwamna Lalong ya ci gaba da cewa ya ji dadi UNDP ta sake kafa wani gidan waya wanda idan wani rikici ya faru koina daga ofis zai san inda al’amarin ke faruwa.

Hukumar tsaro ta Operation Rainbow an kafa ta ne domin karfafa cibiyoyin samar da tsaro a jihar da kare lafiyar al’umma da dukiyoyinsu. Jami’anta dake cikin kananan hukumomin jihar suna taimakawa jami’an tsaro ne da bayanan da zasu taimakesu dakile duk wani tashin hankali.

Shugaban hukumar tsaron farin kaya ta Operation Rainbow Manjo Janar Stephen Guar mai ritaya ya ce Majalisar Dinkin Duniya ce ta taimakwa jihar da dandamalin domin inganta tsaro.

A cewarsa an yi dandamalin ne domin tattaro rahotanni daga karkara dangane da abubuwan da aka ga zasu iya tada hankalin jama’a. Mutanen karkara na iya tura rahotonsu ta kafar sada zumunta. Zasu shiga karkara su wayar da kan jama’a kana su basu kananan wayoyi da zasu yi anfani dasu.

Zainab Babaji nada karin bayani a rahoton data aiko

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Filato Ta Samar Da Dandamalin Inganta Tsaro – 3’ 27”