Gwamnatin jihar Filato da ke tsakiyar arewacin Najeriya ta musanta labaran da ake yadawa musamman a kafafen sada zumunta, wadanda ke cewa an kai hari kan wasu motocin safa a Jos.
Wata sanarwa da Darektan yada labaran jihar Dr. Makut Simon Macham ya fitar, ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da labaran domin babu gaskiya a ciki.
“Muna kira ga jama’a da su yi watsi da rahotannin da ke bayyana a shafukan sada zumunta wadanda suka nuna wasu motocin bas-bas suna cin wuta, inda ake cewa rikicin Filato ya ta’azzara yayin da aka kona motocin bas na luxurious da ke dauke da fasinja 'yan kabilar Igbo 156. Wadannan rahotanni na kanzon kurege ne, babu abu makamancin wannan da ya faru.” Sanarwar Dr. Macham ta ce.
“Wannan aiki ne na masu rura wutar rikici, wadanda suke so su haifar da rudani don a ta da husuma tare da jefa tsoro a zukatan jama’a.”
Hukumomin jihar ta Filato sun kara da cewa, tuntuni, al’amura sun daidai, kuma an shawo kan matsalar tsaron jihar.
“An tura jami’an tsaro a duk sassan Jos don su tabbatar ana bin dokar hana fita ta sa’a 24 wacce har yanzu tana aiki.”
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya ba jami’an tsaro umarni, su bi diddigi tare da kama wadanda suke yada ire-iren wadannan labarai na karya, wadanda burinsu shi ne, su haddasa fitina.
“Muna kira ga jama’a da su guji yada labaran kanzon kurege domin za su iya haifar da mummunan sakamako ga wadanda ba su ji ba ba su gani ba.”
A ‘yan kwanakin nan, birnin Jos ya sake fadawa kangin rikicin da ake dangantawa da addini da kabilanci, tun bayan da aka tare wasu matafiya da dama aka kashe su a yankin Rukuba Road da ke Gada Biyu a Jos ta Arewa.
Kwanaki kadan bayan wannan hari, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yankin Yelwan Zangam a Jos ta Arewar, inda suka kashe mutane da dama, lamarin da ya kara dagula al’amuran tsaro har ya sa hukumomi suka maido da dokar hana fita ta sa’a 24 duk da cewa an sassauta ta a baya.