Wannan dai ya kawo kasar ta Colomboia kusa da karshen yakin shekaru 50 da suka kwashe suna yi tsakanin su wadannan ‘yan tawayen dake sari ka noke da kuma ta'addan ci.
Shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos da shugaban FARC Rodrigo Londona Echeveri sun sa hannu a babban birnin Havana inda suka kwashe shekaru 4 suna kiki kaka domin cimma matsayar zaman lafiya.
Shugaban kasar Cuba Raul Castro da Ministan harkokin wajen Norway Borge Brende wadanda kasashen su ne suka yi ta kokarin ganin shiga tsakani, suna cikin tawagar da suka sa ido wajen wannan bikin rattaba hannu ciki ko harda sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban-ki Moon, dama tawagar Amurka karkashin jagorancin Benard Aroson dama dai shugabannin wasu kasashen kudancin Amurka.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya bada sanarwa, yana cewa dakatar da wannan bude wuta abu ne da ake maraba dashi ba ga mutanen kasar Colombia kawai ba a’a ga dukkan wani mai son zaman lafiya.
A cikin jawabin na Kerry yace kasar Amurka dai ta taimakawa kasar ta Colombia domin ganin ta karfafa demokaradiyyar ta kana ta inganta matakan tsaron mutanen ta, yace wannan kyakkyawar danganta tsakanin kasashen biyu zaici gaba.