Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan adawan Venezuela na cigaba da kokarin tsige shugaban kasar


Shugaban Venezuela Nicholas Madura dan kwaminisanci
Shugaban Venezuela Nicholas Madura dan kwaminisanci

‘Yan adawan kasar Venezuela sun ce sun shigar da koke ga hukumar zaben kasar game da kiran a yi zaben raba gardama a duk fadin kasar don neman tsige shugaban kasar Nicolas Maduro.

Gamayyar ‘yan adawan da suka gana a jiya Litinin sun ce, sun tattaro sa hannun mutane sama da Miliyan Daya Da Dubu Dari Takwas Da Hamsin, fiye da ninki tara na yawan yadda ake bukata don aiwatar da zaben raba gardama.

Jam’iyyun sun kushe salon mulkin Shugaba Maduro game da karancin abinci da magunguna, da tashin farashi da kuma karuwar daukewar wutar lantarki a kasar. Dole hukumar zaben ta tabbatar da sa hannun da aka samu.

Sannan ‘yan adawar na iya kokarin samun kaso 20 na sa hannun zaben, akalla kimanin mutane Miliyan 4 kafin zaben raba gardamar ya wakana.

Zaben jin ra’ayin da aka yi kwanan nan ya nuna cewa kaso 2 cikin 3 na mutanen Venezuela na son Maduro ya bar mukaminsa na shugabancin kasar.

XS
SM
MD
LG