Duk da hakan ministan yace cikin wannan makon za'a fitar da bayanan wadanda aka samu da laifin almundahana koda ba za'a ambaci sunayensu ba.
Wani mai sharhi akan lamuran yaki da cin hanci da rashawa Bashir Baba yace bayanin ministan haka yake domin shugaban hukumar EFCC Mr. Magu yace duk wanda ta kira to da wuya a ce bashi da hannu a cin hanci da rashawa. Da wuya a ce bashi da wani tabo a cikinsa. Amma duk da haka sai a bari kotu ta tabbatar cewa wanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa ya aikata laifin.Kotu ce zata tabbatar da barayin.
Dangane da wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban kasa cewa ranar Alhamis din nan mai zuwa za'a ga wasu sunaye sun fito, Bashir Baba yace sai a tsaya a ga wadanne sunaye ne zasu fito. Yace akalla dai an san akwai wadanda EFCC ta sa gaba kuma sun mayar da wasu kudade. Kuma duk wanda ya maida kudi to ya amsa ya tafka dan hali. Idan an bayyana sunayen irin wadannan babu laifi.
Kungiyar kwadagon Najeriya tace bata goyon bayan rufawa duk wani mai zarmiya asiri. Shugaban kungiyar Ayuba Wabba yace tun lokacin soja suke gwagwarmaya da cin hanci da rashawa. Kungiyar bata boyewa, duk inda akwai cin hanci da rashawa zata fada.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5