Dan Majalisa Isa Sarkin Adar yace kasar ba shari'ar musulunci ake yi ba amma akwai dokar yanke hukunci kisa wa wadanda aka kama suna fashi da makami.
Yace a wurinsa yanzu laifin sace mutane ana garkuwa dasu ya fi fashi da makami muni.'Yan fashi da makami idan sun sami kudi wurin mutum zasu sakeshi amma masu sace mutane koina suka samu mutum zasu tilastawa 'yanuwan mutumin su biya kudin fansa ko kuma su kashe mutum. Tabbas wannan ya fi muni. Saboda haka majalisar wakilai zata yi na'am da ita.
Matsalar sace mutane domin neman kudin fansa da ta ta'azara a kudancin kasar yanzu ta yadu zuwa arewaci kuma tana neman zama ruwan dare gama gari.
Wani zubin sace mutane ya wuce neman kudin fansa idan aka yi la'akari da kashe Kanar Inusa a Kaduna da rundunar soja tace tun ranar da aka saceshi aka hallakashi.
Kungiyar kare 'yancin dan Adam ta Amnesty International na kira a soke dokar hukuncin kisa tare da cewa hakan ba zai hana aikata laifuka ba.
Ambassador M.K.Ibrahim yace doka ce wadda take dole a tsaya a yi nazari a kanta sosai. Anfanin doka da hukunci shi ne a tabbatar an rage yin laifi. Amma idan hukuncin da ake zartaswa baya rage laifi sai ma kara harzukashi ya keyi to dole a tsaya a yi nazari. Misali idan aka soma kashe masu satar mutane babu tabbacin su ma ba zasu fara kashe mutane ba.
Ga karin bayani.