Gwamnatin Buhari Nada Karin Bayani Kan Kudaden Sata da Take Cigaba da Kwatowa

Shugaban gwamnatin Najeriya Muhammad Buhari

Yaynida 'yan Najeriya ke korafi kan yawan kudaden da aka ce an kwato daga hannun barayinta sun yi kadan, kuma basu burge 'yan Najeriya ba, ministan yada labaran kasar yace daga yanzu 'yan kasar zasu dinga samun karin haske domin ana cigaba da kwato kudin.

Ministan yace kudaden suna cigaba da shigowa aljihun gwamnati lokaci zuwa lokaci.

Abun da gwamnati ta bayyana ba duka ba ne domin suna shigowa ta hanyoyi daban daban.

Shi ma shugaban hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ko EFCC, Ibrahim Magu, yace ko kadan basu gamsu da adadin da gwamnati ta bayyanawa 'yan kasar ba saboda ana fada kukaden kuma na cigaba da shigowa ta wata hanyar. Yace sabili ke nan da ministan labarai Lai Muhammed ya yi gyara.

Ibrahim Magu yace nan gaba ministan zai kara bayyanawa 'yan jarida adadin kudaden da suka shigo hannun gwamnati daga barayin biro. Yace ba EFCC kadai ke kwato kudaden ba. Akwai ma'aikatar shari'a ta tarayya. Akwai ICPC da ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ko NSA da dai sauransu.

Dangane da kadarorin cikin gida da na kasashen waje da barayin suka mallaka , Ibrahim Magu yace odar da ma'aikatar shari'a ta bayar ta taimaka domin barayin ba zasu iya sayar dasu ba saboda haka suna nan suna aiki a kansu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Buhari Nada Karin Bayani Kan kudaden Sata da Take Cigaba da Kwatowa - 3' 40"