Wata sanarwa da ministan yada labaran kasar Alhaji Lai Muhammed ya fitar a Legas a yau, ta nuna cewa gwamnatin har ila ya ta kwato wasu miliyoyin dalolin kudin pam na Ingala daga tsoffin jami’an gwamnati da sauran ‘yan siyasa.
Ya ce an kwato kudaden ne tsakanin ranar 29 ga watan Mayun bara zuwa 25 ga watan Mayun bana.
Yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin batutuwan da shugaba Buhari ya yi alkawarin zai yaki da su musamman a wannan lokaci da Najeriya ta ke fadi tashin neman kudaden shiga.
A bikin cika shekara guda da kafa gwamantin nan a karkashin jam’iyar APC, mutane suka zura ido su ji an bayyana sunayen mutanen da aka kwato kudade a hannunsu, kamar yadda gwamnati ta yi alkawari a baya. sai dai hakan bai yiwuwa ba, lamarin da ya janyo cecekuce a tsakanin ‘yan Najeriya.
Wata babbar badakala da gwamnatin ta Buhari ke bincika a yanzu ita ce ta sayen makaman da ya kamata a yaki kungiyar Boko Haram daga ofishin tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, wato Kanar Sambo Dasuki.
Domin jin cikakken adadin kudade musamman na nairori da daloli da kuma pam-pam na Ingila da aka kwato, saurari rahoton wakilin Muryar Amurka, Babangida Jibril daga Legas: