Gwamnatin Borno Tayi Watsi da Kiran a Dage Zabe Zuwa Watan Satumba

Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima.

Kwanan nan wasu jam'iyyu 23 a jihar Borno suka kira a dage zabe har zuwa watan Satumba

A firar da wakilin Muryar Amurka yayi da mataimakin gwamnan Borno Alhaji Zanna Umar Mustapha ya shaida mashi cewa gwamnatin jihar bata goyi bayan kiran ba.

Mutanen da suka yi kiran mutane ne da basu da kowa. Mutane ne dake zaune suna jiran irin wannan lokacin domin a basu wani abu. Kiran da suka yi bai kamata ba kuma baya kan tafarkin dimokradiya.

Yace abun da dimokradiya ta tanada shi ne a yi zabe lokacin da doka ta tsayar a yi.Doka ta shirya cewa kowace shekara hudu za'a yi zabe. Babu a tsarin mulkin Najeriya inda aka ce a dage zaben daga lokacin da yakamata a yi shi.

A jihar Borno kowane lokaci aka yi zabe jam'iyyarsu ta APC ita ce zata ci. APC ita ce jam'iyya dake kan gaba a jihar. Wanda yayi magana ra'ayinsa ne. Wai yana ganin idan an dage zaben zai samu dama yayi abun da yake son yayi.

Wadanda suka yi kiran suna ganin har yanzu akwai tashin hankali a jihar kuma bai kamata a yi zabe a irin yanayin ba. Mataimakin gwamnan yace ai kasar Afghanistan ta fi Najeriya yawan tashin hankali kuma an gudanar da zabe. Yace batun rashin zaman lafiya batu ne na shugabancin kasa. Shugaban kasa ya kamata ya tabbatar da tsaro tun lokacin da aka fara rikicin. Shugaban kasa ya san lokacin zabe zai zo.Kuma ba'a yi komi ba sai da aka shiga cikin halin kakanikayi. Yace to amma tunda yanzu yace za'a gama cikin sati shida suna kai. Sun kwato kananan hukumomi 5 daga cikin 17 dake hannun 'yan Boko Haram. Shi shugaban kasa ya kai ziyara Borno inda yayi alkawarin kawo karshen tashin tashinar cikin makonni biyu nan gaba.

Mataimakin gwamnan ya kara da cewa duk wanda ya zabi PDP ba mutum ba ne mai cikakken hankali. A zaman kunci da suka yi cikin shekaru uku da rabi bai kamata a ce PDP ta ci komi ba domin tun da can bata taba cin zabe a Borno ba. Rashin zaman lafiya ya yiwa jihar katutu har ma daga karfe shida na yamma dole su shige jidagensu kamar kaji. Wanene ya kawo rashin zaman lafiya. Yace su basu ce Jonathan ne ya kawo Boko Haram ba amma da kungiyar ta taso me ya sa ba'a dakileta ba tun kafin ta habaka? Yace 'yan Boko Haram 'yan Borno ne da wasu suka hadu suka kafa kungiyar, suna karantawa da fasara Kur'ani yadda suka ga dama. Sabili da haka yakamata sha'anin PDP ya fita daga ran mutumin Borno.

Ga rahoton Haruna Dauda Biyu.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Borno Tayi Watsi da Kiran a Dage Zabe Zuwa Watan Satumba - 3' 31"