Gwamnatin Borno Ta Rabawa Marasa Aikin Yi Tasi, Keke Napep Da Bas 610

Motocin tasi da gwamnatin jihar Borno ta kaddamar (Hoto: Gwamnatin Borno)

Hukumomin jihar sun ce kowane Keke Napep na dauke da wani tambarin na’ura da zai rika bibiyar duk inda aka je da abin hawan da zimmar tabbatar da ana amfani da shi bisa ka’ida.

Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta kaddamar da motocin tasi, Keke Napep da bas-bas 610 don inganta fannin sufurin jihar.

A ranar Alhamis Gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar da motocin wadanda suka hada da tasi kirar Toyota LE guda 100 da Keke Napep 500 da kuma motocin bas-bas kirar Ashok Leyland guda 10.

Motocin bas din masu cin fasinja 41 ne kamar yadda gwamnatin jihar ta Borno ta sanar a shafinta na Facebook a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce za a bar motocin bas din karkashin kulawar hukumar sufurin jihar ta Borno Express don yin aiki a cikin birni.

Sannan Keke Napep din guda 500 an mika su ga mutum 2000, inda kowane Napep guda aka ba mutum hudu da ba su da aikin yi don su kula da shi.

Kazalika motocin tasin guda 100 an mika su ga mutum 200, inda mutum bi-biyu za su rika kula da kowace tasi daya.

Hukumomin jihar sun ce kowane Keke Napep na dauke da wani tambarin na’ura da zai rika bibiyar duk inda aka je da abin hawan da zimmar tabbatar da ana amfani da shi bisa ka’ida.