Kwamishanan ma'aikatar shari'a ta jihar kuma Antoni Janar Barrister Kaka Shehu Lawal ya bayyana matsayin da gwamnatin jihar ta dauka ga taron manema labarai da ya kira.
Inji kwamishanan gwamnatin ta dauki matain ne domin tabbatar cewa kwarya kwaryar zaman lafiyan da aka samu ya dore. An baiwa masu sana'ar da yanzu ta zama haramtata wa'adin zuwa ranar ishirin ga wannan watan su kwashe nasu-inasu su fice ko kuma doka ta hau kansu.
Amma dokar hana sayarda barasa bata shafi barikokin 'yansanda da na sojoji ba. Baicin wadan nan wuraren duk wanda aka kama yana aikata laifin za'a kamashi a kuma hukumtashi.
Haka ma masu sayarda gayawayi da itacen girki an gargadesu su koma wurin da aka kebe masu idan kuma suka ki doka ta hau kansu. Kazalika an kuma rufe wasu tasoshin motoci cikin jihar da gwamnati bata san da zamansu ba.
Kwamishanan shari'a yace domin an fara samun zaman lafiya mutane suna shan giya kuma su yi fada bayan sun bugu. Yace kullum sai an samu rahoton an soki wani da wuka kuma ya mutu. Saboda haka ya zama wajibi su hana.
Gidajen karuwai sun fara bullowa inda 'yan iska suke taruwa har ma an fara saye ko sayarda jarirai kan Nera dubu dari. An kama wasu kuma an gurfanar dasu gaban kotu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5