Gwamnatin Amurka Ta Musanta Zargin Cin Zarfin ‘Yan kasar Haiti

Your browser doesn’t support HTML5

Wannan lamari ya sa wakilin Amurka na musamman a Haiti ya ajiye aikinsa yayin da ake sukar matakan da gwamnatin Biden ta dauka akan bakin hauren.
Gwamnatin Biden ta musanta zargin da ake yi mata akan ‘yan ciranin Haiti, bayan da wakilin Amurka na musamman a Haiti ya yi murabus, inda ya soki gwamnatin Shugaba Joe Biden saboda abin da ya kira "rashin mutunta hakkin dan Adam" da "daukar matakai mara sa kyau" akan dubban 'yan ciranin Haiti da suka yi dandazo a kan iyakar kudancin Amurka. Wakiliyar Muryar Amurka a Fadar White House, Patsy Widakuswara na dauke da rahoton.