Ma’aikatar Shara’a ta Amurka tace zata dauki wani matakin da Atone-janar na Amurka, Jeff Sessions ya bayyana da cewa na” ba saban bane” na neman babar Kotun Kolin Amurka ta kawar da hukuncin da wata karamar Kotun Daukaka Kara ta jihar California ta yanke, inda ta hana wa Gwamnatin Tarayya ja wa shirin bada kariya ga matasan da aka zo da su Amurka tun suna kananan yara burki, shirin da ake kira DACA.
A jiya talata ne gwamnatin shugaba Donald Trump ta bada sanarwar niyyarta na neman Kotun Koli ta sake nazarin wancan hukuncin.
Ana daukar matakin akan na “ba saban” ba ne da yake gwamnatin tarayya ta bayyana niyyarta na chanja shirin DACA din tun ma kafin ita wancan Kotun Daukaka Kara ta birnin San Fransisco ta kamala yanke nata hukunci.
Atone-Janar Sessions ya gabatarda hujjar cewa hukuncin wancan kotun hukunci ne da “hankali ba zai dauka ba kuma ya sabawa doka”, musamman ma ace “wai alkali guda daya zai iya yanke hukuncin da zai shafi kasa baki daya kan shirin na DACA.