Gwamnati Zata Biya ASUU Naira Biliyan 30 Nan Da Watan Nuwamba

Kungiyar ASUU

Gwamnatin Tarayyan Najeria ta amince ta biya ASUU bashin naira Biliyan 30 daga cikin abinda take bi kafin 6 ga Nuwamba

Gwamnatin Tarayyan Najeriya da Kungiyar ASUU sun cimma yarjejeniyar biyan Naira Biliyan 30 daga cikin alawus da kungiyar ke bin gwamnati a yayin zama da aka yi da wakilan kungiyar da bangaren gwamnati.

A wajen taron, Ministan Kwadago da Ayyuka, Dr. Chris Ngige ya ce Gwamnati ta sha alkawarin biyan kudi naira Biliyan 40.

Yayi bayani cewa, za’a fara biyan Biliyan 30 a cikin Biliyan 40 din da suke bi kafin 6 ga Nuwamba, sauran Biliyan 10, za a bayar da su a kashi biyu.

Na farko, acikin watan Mayu, 2021 sai kuma kashi na biyu a da za’a bayar a cikin watan Feburairun 2022.

Shugaban Kungiyar ASUU na Kasa, Biodun Ogunyemi, ya roki gwamnati da ta dauki wannan batun a matsayin matsalar dake bukatar gaggawa, ganin cewa, harkar ilimi a kasar nan ta na bukatar kulawa ta gaggawa.

Za’a ci gaba da tattaunawar a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoba, bayan kungiyar ta tattauna da mambobinta game da hukuncin da suka cimma.

Wadanda suka halarci taron sun hada da karamin ministan kasa, aiki da daukar ma’aikata, Festus Keyamo SAN; shugaban zartaswa na hukumar biyan albashi, Ekpo Nta; Sekataren din-din-din na ma’aikatar ma’aikata da daukar ma’aikata, Dr Yerima Peter Tarfa, da sauransu.