Gwamnati Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Akan Saran Itace

Hamada

Hukumomi a Nijar na cigaba da fadakarwa gameda bala'in da ke cikin sha'anin gurgusowar hamada musamman ganin cewa kashi 2 bisa 3 na kasar dukkan hamada ce ta mamaye shi.

A yau ne take ranar yaki da gurgusowar Hamada a dukkan fadi duniya, ganin cewa kowace shekara wurare da dama ne Hamada ke mamayewa a kasashen duniya daban daban.

A Kasar Nijar, kashi biyu cikin uku na fadin kasar ne Hamada ta mamaye shi yasa hukumomi a kasar ke cigaba da fadakar da al’uma domin bada tasu gudunmuwa wajen yaki da gurgusowar Hamada.

Daya daga cikin jami’an ma’aikatar gandun daji kasar ta Nijar, Musa Habu, ya ce ma’aikatar gandun daji ta dukufa wajen dashen itatuwa da kuma wani salon gina manyan ramuka domin tara ruwa idan damuna ta sauka domin a samun na ban ruwan dashebn da aka yi.

Dahiru Bala, wani dan kasar ta Nijar cewa yayi batun Hamada kam ta shafi al’umar kasa domin a cewarsa abinda ya kama daga Agadez, zuwa Libiya har kasar Algeria Hamada ce idan da wannan hanyar akwai tsire da albarkar da za a samu a kasar Nijar Allah kadai yasa iyaka.

Hukumomin kasar ta Nijar sun tanadi hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama ya sari itace ba tare da izini ba.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnati Ta Tanadi Hukunci Mai Tsanani Akan Saran Itace - 3'08"