Gwamnati Ta Dakatar Da Twitter A Najeriya

Ministan yada labarai Lai Mohamed.

Jama'a da dama na ganin, Najeriya ta dauki wannan mataki ne a matsayin martani ga goge sakon Shugaba Buharu da kamfanin ya yi a ranar Laraba.

Hukumomin Najeriya sun dakatar da shafin Twitter a kasar, a wani mataki da ake ganin martani ne kan goge sakon shugaban kasar da kamfanin ya yi a farkon makon nan.

Twitter ya goge wani sako da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a ranar Laraba, wanda ke yin gargadi ga masu ta da kayar baya a yankin kudu maso gabashin kasar, inda ya yi nuni da irin asarar rayuka da Najeriyar ta yi a lokacin yakin basasa.

“Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta dakatar da Twitter a Najeriya har sai baba ta gani.” Wata sanarwa da Segun Adeyemi wanda ke magana da yawun ministan yada labarai Lai Mohamed ta ce, kamar yadda kafafen yada labarai da dama suka ruwaito a kasar.

Sanarwar ta ce, daukan matakin ya zama dole, saboda amfani "ana yawa amfani da shafin wajen gudanar da wasu ayyukan da ka iya yin barazana ga zaman lafiyar Najeriya."

Karin bayani akan: Twitter, IPOB, INEC, Shugaba Muhammadu Buhari, Lai Mohamed, Nigeria, da Najeriya.

Sai dai sanarwar ba ta ambaci lokacin da matakin zai fara aiki ba.

A ranar Laraba Lai Mohamed ya zargi Twitter da yin biris da kalaman da shugaban kungiya IPOB, Nnamdi Kanu da magoya bayansa ke wallafawa a Twitter, amma ya mayar da hankali kan na Buhari.

Hakan ya sa ministan ya yi nuni da cewa, suna zargin kamfanin na Twitter na goyon fafutukar IPOB.

“Kungiyar da take ba mambobinta umarnin su kai hari kan ofisoshin ‘yan sanda, su kashe ‘yan sanda, su kai hari gidan yari, su kashe gandurobobi, sai kuma a ce shugaban kasa ba shi da ikon ya nuna fushinsa? Mohamed ya fadawa manema labarai a Abuja a ranar Laraba, kamar yadda kafafen yada labaran kasar da dama suka ruwaito.

Lai ya kara da cewa, “Twitter na da ka’idojinta, amma ta kwan da sanin cewa, ba ka’idoji ba ne na duniya, duk shugaban kasar da ya ga wani abu da bai kwanta masa a rai ba, yana da ‘yanci ya bayyana ra’ayinsa.”

Shi dai Twitter ba ya bari a wallafa kalaman batanci ko wadanda za su tunzura mutane su ta da rikici.

A farkon shekarar nan, kamfanin ya rufe shafin tsohon shugaban Amurka Donald Trump saboda abin da ya kira kalamai da yake wallafawa masu iya ta da hankali.

Wannan takaddama na zuwa ne, kasa da wata biyu bayan da kamfanin na Twitter, ya ayyana cewa zai bude hedkwatarsa ta yankin nahiyar Afirka a Ghana, lamarin da ya fusata 'yan Najeriyar da ma hukumomin kasar.

An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Your browser doesn’t support HTML5

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi