Gwamnan Taraba Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Kisa Ga Masu Garkuwa

Gwamnan Jihar Taraba, Darius Dickson

Wannan matsalar ta garkuwa da jama’a yanzu haka na hana jama’a barci a Najeriya, lamarin da yasa magidanta da dama kauracewa gidajensu idan dare yayi.

A kokarin da gwamnatoci su ke yi don shawo kan lamarin yasa ‘yan majalisar dokokin jihar Taraba, da aka taba sace wani abokin aikinsu dan majalisa wanda daga bisani aka kashe shi, daukan mataki na kafa dokar kisa ga duk wani da aka kama yana garkuwa da mutane, kuma tuni har gwamnan jihar ya rattabawa dokar hannu.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar, Hon. Bashir Muhammad Bape, ya ce yanzu a jihar ta su idan dai aka kama mutum ya yi garkuwa da mutum don neman kudin fansa ko tsoratarwa to hukunci kisa ya haushi.

Shi ko da yake tsokaci game da matsalar tsaro, musamman a jihar Taraba, tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar kuma yanzu jakadan Najeriya a kasar Trinidad da Tobago, Ambassada Hassan Jika Ardo, ya ce dole al’umman jihar su tashi tsaye a bisa abun da ya kira shakulatin bangaro da kuma rikon sakainar gwamnatin jihar ga halin ni ‘yasun da al’umma ke ciki.

Yanzu haka a jihohin Adamawa da Taraba, da wuya a wayi gari ba tare da rahoton an yi garkuwa da wani, ko wata ko wasu ba. Kuma wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu jihohi a Najeriya ke gayyatar ‘yan sa kai da maharba don kai musu dauki.

Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz daga Jalingo:

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Taraba Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Kisa Ga Masu Garkuwa Da Mutane