Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya ce wulakancin da wasu matasan Bidda suka yi masa a lokacin da ya je jajen gobarar da ta lakume kasuwar Biddan makon jiya wasu ne suka shirya shi saboda dalilai na siyasa.
A makon jiyan ne gungun matasan suka yiwa tawagar gwamnan ature da kasa da jifa da duwatsu tare da wasu kalamai na batanci bayan da ya mika Nera miliyan 20 ga wadanda abun ya shafa a matsayin tallafin farko.
A cewar gwamnan, kazalika abun da ya faru shiryashi aka yi amma ba matsayin mutanen Bidda ba ne. Injishi ya yi babbar sa'a akan mutanen Bidda saboda tsohon gwamna Abdulkadir Kure a karshen wa'adinsa na mulki bai sha da dadi ba a Biddan. Haka ma gwamnatin da ta gabata saboda a wa'adinta na farko jami'anta basu ma iya zuwa garin.
Gwamnan yana magana ne a lokacin da tawagar matasan jam'iyyar APC daga Bidda ta kai ziyarar bada hakuri akan abun da ya faru.
Alhaji Saidu Ndagi shugaban matasan ya ce sun zo ne su tabbatar masa kada ya yi shakkar goyon bayan Bidda gareshi. Injishi 'yan tsageru ne kawai suka yi aika aikar.
Baba Alhaji Usman shugaban matasan Nupawa, shi ma ya ba gwamnan hakuri.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5