Gwamnan Legas Ya Samarda Motoci da Jiragen Sama Domin Inganta Tsaro a Jihar

Irin cunkoson motoci dake faruwa a Legas da kan taimakawa masu fashi da kwace a rana tsaka.

Sata da fashim da makami da kwace akan hanyar motoci cikin garin Legas ya zama ruwan dare gama gari dalili kenan da gwamnan jihar ya yi wani yunlurin inganta tsaro ta hanyar samarda kayan aiki.

Ayyukan ta'adanci na karuwa a jihar Legas har ma mujallar The Economist da ake bugawa a birnin London tace lamau ne na gazawar sabon gwamnan jihar Akinwumi Ambode.

A wani mataki na magance matsalar gwamnan ya mayarda martani ne da kaddamar da wasu motocin sintiri fiye da dari shida da jiragen sama masu saukan angulu guda uku domin marawa jami'an 'yansanda baya domin su dakile fashi da makami da kuma kashe kashe na 'yan daba.

Gwamnan yace kudurinsu shi ne su maida Legas birni mai cike da tsaro da tsafta da kuma samarda yanayin saka jari na kowa da kowa. Haka kuma mutane su samu walwala da walawa ba tare da jin tsoro ba.

Mazauna birnin na Legas sun yi na'am da matakin da gwamnan ya dauka. Sun ce matakin nada kyau ga 'ayan Najeriya musamman mazauna birnin.

To saidai wani yace harkar tsaro a Legas ta wuce na bada kayan aiki kawai. Malam Huseni yace ba motocin yakamata a ba jami'an tsaro ba sun 'yansandan yakamata su canza hali tare da kara kaimi wajen aikinsu.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnan Legas Ya Samarda Motoci da Jiragen Sama Domin Inganta Tsaro a Jihar - 3' 04"